Hujjoji daga Littatafan da Aka saukar (Qur’āni da Hadisi) akan Wajibcin Ji da kuma Biyayya ga Shuwagabannin Musulmai
Allāh Yana faɗa cewa:
“Yaku waɗanda suka yi imāni! Ku yi ɗa’a ga Allāh, kuma ku yi ɗa’a ga ManzonSa, da ma’abota al’amari (Shuwagabanni na Mulki da Manyan
Malamai) daga cikinku.” [Surah an-Nisaa’ 59]
(An Karɓo) daga Ibn ‘Umar daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:
“(Wajibi ne) akan mutum musulmi ji da
biyayya a cikin abin da yake ƙauna da abinda baya ƙauna sai dai in an umurce shi da (aikata) saɓo, idan aka umurce shi da (aikata) saɓo, Babu
ji da biyayya.”
Daga Ibn ‘Umar yace:
“Mun kasance idan mukayi mubaya’a da manzon Allāh tsira da aminci su tabbata a gare shi akan jī da biyayya. Sai yace mana:
“gwargwadon cikin abunda zaku iya”.
Kuma daga Ibn ‘Umar yace: Naji Manzon Allāh tsira da amincin Allāh su tabbata a gare shi, yana cewa:
“Dukkan wanda ya cire hanunsa daga biyyaya (ga Shuwagabanni) zai hadu da Allāh ranar tashin alkiyama bashi da hujja, haka duk wanda ya mutu alhali bai yi mubaya’a ba, to lallai yayi mutuwa irin ta jahiliyyah.”
Manzon Allāh (tsira da aminci su tabbata a gare shi) yace:
“Mafifici daga cikin shuwagabanninku su ne waɗanda kuke ƙauna, Suma suna kaunarku, waɗanda suke maku addu’a, kuma kuna masu addu’a. Mafi Muni daka cikin shuwagabanninku sune waɗanda kuke jin haushin su, suma suna jin haushin ku, Kuna la’antarsu, suma suna la’antarku.”
Sai wani yayi tambaya:
“Ya manzon Allāh, shin baza mu yaƙe su ba?” Sai manzon Allāh tsira da amincin Allāh su tabbata a gare shi yace:
“A’a, matuƙar suna tsayar da sallah. Idan kuka ga wani abu daga cikin ayyukansu abin da kuke ƙyamata, ku ƙyamaci aikin nasu, Amma Kada kuyi masu fito-na-fito”.