Mafi Girman Nagartar Al-ƙur’āni (Na Babban Malamin Al Allamah Sālih bin Fawzan Al Fawzan Allāh ya kiyaye shi )
Majiya: Tadabburin Al-ƙur’āni
Da sunan Allah Mai Rahma Mai jinƙai
Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga mahaliccin talikai. Tsira da aminci su tabbata akan manzonSa annabinmu Muhammad da ahalinsa tare da sahabbansa kuma Ya ƙara tsira mai yawa a garesu.
Bayan haka;
Lallai mafi girman ni’imah da Allāh ya karrama wannan al’ummah da ita, ita ce aiko annabi Muhammad sallAllaahu ‘alayhi wa sallam da saukar masa da Alƙur’ani mai girma, domin shiryar da mutane da (ilmantarda su)wayar da su da tunatarda su dangane da abubuwan da zasu amfanar dasu a cikin wannan duniya da lahira.
Lallai Al-ƙur’āni magana ce ta Allah, da harufansa da ma’anoninsa, saukakke (daga sama) ba halitta ba ne, daga wurin Allah ya fito kuma zuwa gare shi yake komawa.
Dalili;
Kuma lallai shi (Al-ƙur’āni), haƙiƙa, saukarwar mahaliccin halittu ne.
Ruhi amintacce(mala’ika Jibril)ne ya saukar da shi.
A kan zuciyarka, domin ka kasance daga masu gargaɗi.
Da harshe na Larabci mai bayani.
(Ash Shu’ara)
A cikinsa shiriya ne da kuma haske.
Allah maɗaukaki Yana cewa;
Da sunan Allāh Mai Rahma Mai jinkai:
AlbarkatunSa sun girmama, kuma alkhairanSa sun yawaita wanda Ya saukar da (Littafi) mai rarrabewa(tsakanin gaskiya da karya) ga bawanSa, domin ya kasance mai gargaɗi ga halittu.
(Al Furqaan-1)
Shi Al-kur’ani littafi ne na talikai – dukkan mutane hatta da aljannu (mai bushara ne da gargaɗi)
Aljannu sun saurari Al-ƙur’āni. Faɗin Allah maɗaukakin Sarki;
“Sai suka ce; Lallai ne mu mun ji wani abin karantawa (Al-ƙur’āni), mai ban mamaki.;
Yana nuni zuwa ga hanyar ƙwarai, saboda haka mun yi imāni da shi ba zamu koma bautawa mahaliccin mu tare da kowa ba.”
(Suratul Jinn-1,2)
Da faɗin Allah maɗaukakin sarki:
Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bawanSa kuma bai sanya karkata ba acikinsa
Madaidaici, domin yayi gargaɗi da azaba mai tsanani daga gare Shi, kuma yayi bushara ga muminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cewa) suna da wata lda mai kyau.
Suna masu zama a cikinta har abada.
Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda suka ce: “Allah yana da ɗa.”;
(Surah Al Kahf-1,4)
Har zuwa karshen ayar.
[Muhādarori A Ɓangaren Aƙida da da’wah mujalladi 2/ 276 – 278]