Articles - Rubuce-Rubuce

Al-ƙur’āni Shiriya ne ga Masu Taƙawa (Na Babban Malamin al-Allamah Sālih bin Fawzan Al Fawzan Allāh ya kiyaye shi)

Kuma haƙiƙa Allāh maɗaukakin sarki ya siffanta wannan Al-ƙur’āni mai girma da siffofi masu girma. Ya faɗa a farkon Surah ta Baqarah wadda ita ce Surah ta biyu a cikin jerin Surorin Al-ƙur’āni bayan Fatiha. Allāh maɗaukakin sarki yake cewa;

Da sunan Allāh Mai Rahma Mai jinƙai

A. L. M
Wancan ne Littafi, babu shakka a cikinsa, shiriya ne ga masu taƙawa.
Waɗanda suke yin imāni da gaibu, kuma suna tsayar da sallah, kuma daga abin da Muka azurtasu suna ciyarwa.
Kuma waɗanda suke yin imāni da abin da aka saukar zuwa gareka, da abin da aka saukar gabaninka, kuma game da Lahira suna yin yaƙini

Allāh ya siffanta shi cewa shirya ne ga masu taƙawa:

Haka kuma ya faɗa a cikin wannan Surah (Al-Baqarah);
Watan Ramadāna ne wanda aka saukar da Al-ƙur’āni a cikinsa yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa.

Sai Allāh ya siffanta a farkon surah cewa shiriya ne ga masu taƙawa, haka Kuma ya ƙara Siffanta shi a cikin Surar cewa shiriya ne ga mutane. Kuma wannan siffa ce gamammiya ga masu taƙawa da waɗanda ba su ba.

Amma su masu taƙawa shiriya ne gare su, wato abin nufi;
Suna masu samun amfani da shi da fa’idantuwa daga gare shi kuma suna samun haskakawa da hasken shi. Amma waɗanda ba su ba(marar taƙawa) shiriya ne gare su, wato abin nufi; cewa lallai Yana bayyana masu tafarkin shiriya. Idan suna masu buƙata wa kawunansu shiriya, to! lallai shiriya ne, wannan na nuni da shiriya (zuwa ga hanyar gaskiya) ga mutane baki ɗaya, haka kuma shiriya ne na Tawfeeqī(wacce take daga Allah keɓantacce ga masu taƙawa kaɗai), waɗanda suka karɓi kira na wannan Al-ƙur’āni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *