Ba wajen kowa ake Ɗaukar Ilimi ba (Shaykh Muhammad ibn Sālih Al-Uthaymeen)
Rubuce-Rubuce sun yawaita kuma a hakan waɗansu daga cikin mutanen babu wanda ya sansu. Ba’a sansu da neman Ilimi ba ko fahimta ta karatu ba. A duk lokacin da suka saɓawa gaskiya suna janyo cutarwa akan gama garin mutane.
A dalili hakan, ina mai bada shawara kada a dauki Ilimi daga wadannan rubuce-rubucen face daga wadanda ana da masaniya game da mashayarsu wato, malamai tabbatattu a cikin Addīni da Ilimi saboda kada mutum ya ɓata. Kamar yadda waɗansu daga cikin magabata ke cewa:
“Lallai wannan Ilimi Addīnin ne, mutum ya kula da (halin) wanda zai ɗauko Addīnin sa a wurin sa.”
Ba matsala bace karama. Ina ganin cewa baya kamata mutum, musamman wanda bashi da cikakken Ilimi, ya samu waɗannan litattafai haka da komawa zuwaga litattafan ma’abota Ilimi waɗanda aka yarda da ilmin su da amanarsu.
Lallai haƙiƙa yazo gareni waɗansu litattafai dana karanta wani sashe daga ciki, zantuttuka wadanda ba daidai suke ba a abinda ya shafi Aqeedah (Ƙudiri) da hadisai masu rauni da ƙarya. Gamagarin mutane da daliban Ilimi ƙanana basa iya riskar wannan kuma basu san shi ba.
Wasiyya Da Shawarwai Ga Ɗaliban Ilimi shafi na 382.