Babu Mai Adāwa Da Shaykh Rabee Fāce Karkatattu
Babban Malamin Hadisi Al-‘Allaamah Muhammad ‘Ali Ādam Al-Ithyobi Allah ya gāfarta masa yake cewa:
Shaykh Rabee’ yana daga cikin jagororin malamai masu bin tafarkin magabata a cikin wannan zamani.
Kuma Ina ƙaunar sa shi ma haka yanā ƙaunā ta. Haka Kuma Ina masa tāke da Shu’bah na wannan zamani. Shin kun san wanene Shu’bah bin al-Hajjāj kuwa? ..
Shaykh Rabee Shu’bah ne a wannan zamani namu kuma masu zargin sa da siffantā shi da tsanani, mu sani cewa an sāmu magabata da aka jefe su da hakan daga cikin malamai. Kuma babu mai adawa(Ko ƙiyayya) da shi face karkatattu (wadanda suka zame daga hanya ta musulman farko)
Sharhi na ilal na at-tirmizhi shafi na 175