Fahimtar Kalmar Salaf (Magabaci) Da Kuma Amfanin
Al-Imām As—Safārīni yana cewa:
«ﺍﻟﻤﺮﺍﺩ ﺑﻤﺬﻫﺐ ﺍﻟﺴﻠﻒ :ﻣﺎﻛﺎﻥ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺼﺤﺎﺑﺔ ﺍﻟﻜﺮﺍﻡ ﺭﺿﻮﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﺍﻋﻴﺎﻥ ﺍﻟﺘﺎﺑﻌﻴﻦ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﺣﺴﺎﻥ, ﻭﺍﺗﺒﺎﻋﻬﻢ ﻭﺍﺋﻤﺔﺍﻟﺪﻳﻦ ﻣﻤﻦ ﺷﻬﺪ ﻟﻬﻢ ﺑﺎﻻﻣﺎﻣﺔ ﻭﻋﺮﻑ ﻋﻈﻢ ﺷأﻧﻬﻢ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﺗﻠﻘﻰﺍﻟﻨﺎﺱ ﻛﻼﻣﻬﻢ ﺧﻠﻔﺎ ﻋﻦ ﺳﻠﻒ , ﺩﻭﻥ ﻣﻦ ﺭﻣﻲ ﺑﺒﺪﻋﺔ ﺍﻭﺍﺷﺘﻬﺮ ﺑﻠﻘﺐﻏﻴﺮ ﻣﺮﺿﻲ , ﻣﺜﻞ ﺍﻟﺨﻮﺍﺭﺝ ﻭﺍﻟﺮﻭﺍﻓﺾ ﻭﺍﻟﻘﺪﺭﻳﺔ ﻭﺍﻟﻤﺮﺟﺌﺔ ﻭﺍﻟﺠﺒﺮﻳﺔ,ﻭﺍﻟﺠﻬﻤﻴﺔ ﻭﺍﻟﻤﻌﺘﺰﻟﺔ ﻭﺍﻟﻜﺮﺍﻣﻴﺔ ﻭﻧﺤﻮ ﻫﺆﻻﺀ» .
(ﻟﻮﺍﻣﻊ ﺍﻻﻧﻮﺍﺭ ﻡ 1ﺹ 20).
Yace:
« Abinda ake nufi da Mazhabar Salaf ita ce: abinda Sahabbai masu daraja (Allāh ya ƙara yarda a garesu) suka tafi a kansa, da manyan Tabi’ai wadanda suka biyosu da kyautatawa, da wadanda suka biyosu, da jagororin addini waɗanda akayi masu shaida da jagoranci(acikin addini) kuma aka san da girman matsayinsu a addini, mutane na gari suka ƙarbi maganarsu na baya ya karba daga na gaba, banda wanda aka jefeshi da wata bid’ah, ko ya shahara da wani laqabin da ba yardajje ba, kamar: Khawarijawa (masu fito-na-fito ko sukar shuwagabannin musulmi), Rafidhawa(Yan Shi’ah), Ƙadariyyawa(masu kore ƙaddara), Murji’awa(masu cire aiki daga cikin Imani), Jabariyyawa(masu korewa bayi mashee’ah), Jahamiyyawa(mabiya Jahm bin Safwan, masu korewa Allāh siffofi gaba ɗaya), Mu’utazilawa(masu kore sifofin Allaah kuma suna cewa al-Qur’āni halitta ne), Karramiyyawa(ma biya Muhammad bin Karrām masu cewa Imani shi ne gaskatawa da harshe kaɗai ba tare da tabbatar dashi a zuci ba), da makamantan wadannan».
(Duba Lawami’ul anwar 1/20).
Al-Imāmu Al-Auzā’iy Allah ya jiƙansa yana cewa:
«اصبر نفسك على السنة، وقف حيث وقف القوم، وقل بما قالوا، وكفّ عما كفوا، واسلك سبيل سلفك الصالح فإنه يسعك ما وسعهم»
(اللالكائي في شرح أصول الاعتقاد ١٥٤/١).
Yace:
«Ka haƙurar da kanka akan (riƙo da) Sunnah, kuma ka tsaya iyakar inda ma’abota Sunnah (wato Annabi da Sahabbai) suka tsaya, sannan ka furta dai-dai abinda suka furta, kuma ka kame daga abinda suka kame (daga garesa), kuma kabi tafarkin Magabatan ka na ƙwarai, domin kaima abinda ya wadace su (wato Sunnah kenan) ya wadace ka».
[Duba Sharhu I’tiqadi Ahlis-Sunnati Wal-Jama’ah na Al-Imām Allalaka’iy 1/154]
Shaikhul Islam Ibn Taimiyyah, Allah ya jiƙansa, yana cewa:
«لا عيب على من أظهر مذهب السلف، وانتسب إليه، واعتزى إليه، بل يجب قبول ذلك منه بالاتفاق، فإن مذهب السلف لا يكون إلا حقا» (مجموعة الفتاوى ١٤٩/٤).
Yace:
«Babu aibi ga wanda ya bayyana mazhabin Salaf (magabata na ƙwarai) sannan ya jingina kansa zuwa gareshi, sannan ya nasabta kansa gareshi, hasali ma ya zama tilas a Karɓi hakan daga gareshi da ittifakin Malamai, domin shi Mazhabin Salaf ba komai bane sai gaskiya!»
(Duba Majmu’atul Fatawa 4/149).