Articles - Rubuce-Rubuce

Ko Yin Inkari Ko Rabuwa

Yin Shiru a nan gaskatawa ne da yarda, wanda za’a kama ka(da laifi) akai.

“Kuma lallai ne Mun saukar maku a cikin Littãfi cẽwa idan kun ji ãyõyin Allāh, anã kãfirce musu, kuma anã izgili da su, to, kada ku zauna tãre da sũ, sai sun shiga cikin wani lãbãri. Lallai ne kũ(idan kuka zauna tare da su) a lõkacin nan misãlinsu kuke. Lallai ne, Allāh Mai tãra munãfukai da kãfirai ne a cikin Jahannama gabã ɗaya.

Al hafidh Al Qurṭubi a cikin littafin sa na Al Jaami’ (5/418) yake cewa;

Dukkan Wanda ya zauna a cikin wani majalisi na saɓo Kuma bai yi masu inkari ba, zai kasance tare da su a cikin laifi daidai da su.
Kuma kamata yayi masu inkari idan suka furta abinda yake na saɓo da aikata shi. Idan baya da ikon yi masu inkari toh abinda yake wajaba akansa ya tashi daga cikin su domin kada ya kasance mai kason rabo a cikin wannar ayah.

Nace (Shaykh Arafāt bin Hasan Al Muhammadi hafidhahullah)
Ka guji kasancewa ɗaya daga cikin masu Rabo a wannan ayah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *