Ma’anar Sunnah da Bidi’ah (Shaykh AbdurRahman Ibn Yusuf Al-Ifriqee)
Yana daga cikin abubuwan da yake lalura a addini; Musulumi ya san siffar sunnah da bidi’ah, da bambancin dake tsakanin su.
Ka sani ya kai ɗan uwa mai karamci, cewa idan aka ce Sunnah a Harshen larabci, ita ce hanya. A Yare na shari’a kuwa: ita ce abinda manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana, kuma ya fassara littafin Allah maɗaukaki da shi, na abinda
Ya Shafi Zantuttuka, ayyuka da tabbatarwa (ta hanyar yin shiru idan an aikata a gaban sa), amma duk wanda ba wannan ba bidi’ah ne.
Sunnah ita ce hanyar da ta cancanta mu bi. Ita ce addinin musulunci wanda babu wanda yake kaucewa daga gare ta face jahili, halakakke ɗan bidi’ah.
Asalin ita wannan kalma ta “Bidi’ah” tana nufin ƙagowa akan wani abu wanda a can baya, babu irin shi.
Daga ciki (akwai) faɗin Allah maɗaukakin Sarki:
“Maƙagin halittar sammai da ƙasa” [Suratul Baqarah 2:117]
Abin nufi; Allah ya ƙagi halittar su wanda a can baya, babu irin ta. Wannan baya dacewa a cikin addini face daga Allah maɗaukakin Sarki. Saboda Shi (Allah) ke da ƴancin aikata duk abinda ya ga dama, kuma Shi ne wanda Ya shar’antar mana addini.
Allah maɗaukakin Sarki Yace:
“Ya shar’anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nūḥ”.[Shu’rah 42:13]
Amma Bidi’ah a Yare na shari’a: ita ce ƙirƙira a cikin addini bayan cikar shi; abin nufi bayan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da khalifofin sa shiryayyu.
Haƙiƙa ma’abota bidi’ah sun sanya ta (ita bidi’ar) a matsayin addini tsayayya, ba ya halatta a saɓa mata, kamar yadda ƴan tijjaniyya suke iddi’a’i da waɗansunsu.