Mace ta fita gidanta da ƙanshin sabulu a jikinta
Shaykh Arafāt Ibn Hasan Al-Muhammadi
Mai tambaya:
Mi nene hukuncin fitar mace tana ɗauke da ƙanshi mai daɗi na sabulu?
Jawabi:
Baya halasta.
Saboda hikima da ke cikin wannan.
Ita ce namiji yaji ƙanshi daddaɗa (daga mace) ya kasance daga sabulu ne, ko turare, ko wane irin abu na turare ne ko ba na turare ba, matukar ƙanshi ne Mai daɗi baya halasta ya isa ga namiji.
Wajibi ne akan mace da ta faɗaka da wannan, kada ta fita sai ta gusar da duk wani ƙanshi mai daɗi(da zai iya fita daga jikinta), daga sabulu ne, ko wani abu. Saboda mi cece hikima aciki? Ita ce ƙanshi Mai daɗi zai iya isa ga namiji sai ya fitinu.
Wannan sai ya zamo sababi na fitina.