Manhaj - Tafarki

Me yasa ake ce masu ahl-us-Sunnah wal Jamā’ah? Shaykh Sālih Al-Fawzān

Ahl-us-Sunnah ana kiran su da wannan taken “ahl-us-Sunnah” saboda suna aiki da Sunnah (tafarkin manzon Allāh tsira da amincin Allāh su tabbata a gare shi) da lazimtar shi.

Haka kuma ana ce masu “Jamā’ah” saboda a haɗe suke, babu rabuwa tsakanin su. Tafiyar su guda ɗaya ce, ita ce littafin Allah da Sunnah. Sun haɗu akan gaskiya haka kuma sun haɗu ƙarƙashin shugaba ɗaya. Dukkan al’amurran sun ginu ne akan haɗin kai, taimakekeniya da soyayya a tsakinin su.

Ahlus Sunnah – Ajwibah Almufeedah, shafi na254.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *