Raddi ga kowace ɓarna wājibi ne Da kuma raddi ga masu cewa ” ka shagaltu da naka aibi”
Babban Malami Shaykh Ibn -Uthaimeen rahimahullah yake cewa:
“Raddi akan ɓata -(wato kō da ya kasance ɓata daga abin da aka ƙirƙira ne na zantuttuka ko na ƙuduri ko na ayyuka)- shi ne abin da ya kamata kuma barin sa (raddin) shi ne aibi.
Idan akace da wanda yake raddin ɓata; ka shagaltu da aibin kanka ka rabu da aibin wasu.
Zā mu basu amsa da cewa; Wannan yana daga cikin aibi nā idan ban yi raddi akan ɓata ba, domin yin raddi akan ɓata, abu ne da yake wājibi”. ¹
¹ Fatḥu dhil jalāli wal ikrām 15/332