Articles - Rubuce-Rubuce

Takaituwa Akan Sunnah Shi Ne Mafi Alkhair

Abdullah bin Mas’ud, Allāh ya yarda da shi yace;
Taƙaituwa akan Sunnah yafi alkhairi da ijtihādi akan Bid’ah (kirkiro abubuwa a Addīni)¹

Haka kuma an Karbo daga Saeed bin- Mussayyib cewa ya hangi wani mutun yana sallah bāyan fitowar rāna sama da raka’o’i guda biyu, yanā yawaitawa a cikin ruku’i da sujudi. Sai (Saeed)ya hane sa. Sai (mutumin) yace;
Ya kai mahaifin Muhammad, shin Allāh zai azabtar dani akan sallah?
Ya amsa cewa: A’a Amma zai azabtar da kai domin sāɓawa Sunnah ²

 

¹ Ad Dārimi ya fitar 223 haka Al lālakā’i 1/55-8

² Al Khateeb ya fitar dashi a cikin Al fiqh wal mutafaqqih 1/147

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *