Biographies - Tarihi

Tarihin Rayuwar Shaykh Muḥammad ibn AbdulWahhāb

*SUNAN SHI*

Shi ne Shaykh Muḥammad Ibn AbdulWahhab Ibn Sulaiman Ibn Ali Ibn Muhammad Ibn Ahmad Ibn Rāshid At-Tameemee.

*HAIHUWAR SHI DA KUMA TASOWAR SHI*

An haife shi a shekara ta 1115 bayan Hijrah (wanda yayi daidai da Shekara ta 1703 miladiyya) a garin ‘Uyaynah, wanda yake arewacin Riyādh.

Ya tashi a hannun mahaifinsa, Shaykh Abdulwahhab, a garinsu; yana daga cikin waɗanda Allāh Yaba baiwa da kaifin basira da jikin girma. Ya haddace Al-ƙur’āni yana ɗan shekara goma, ya kuma manyanta a shekara sha biyu

*MALAMAN SHI*

Yayi karatu a wajen mahaifin shi a garin ‘Uyaynah, sai ya cigaba da karatu a wajen Malaman Najd, Al-Ahsa, Al-Basrah da sauran su.

Daga cikin malaman shi akwai:

– Mahaifinshi, Shaykh AbdulWahhab ibn Sulayman
– Shaykh AbduLlah ibn Ibrahim Ibn Sa’id Aal As-Sayf An-Najdee
– Shaykh Muhammad Hayaat As-Sindee
– Shaikh ‘Alee Afendee ad-Daaghistaanee
– Shaikh Ismaa’eel al-‘Ajloonee
– Shaikh ‘Abdul-Lateef al-‘Afaaliqee al-Ahsaa’ee

*LITTATAFAN SHI*

Shaykh Muhammad ibn AbdulWahhab ya wallafa littattafai da dama a fannoni da kimiyyar musulunci, wasu daga cikin su akwai:

– Kitāb At-Tawheed
– Usool Ath-Thalāthah
– Al-Qawa’id Al-Arba’
* Fadl Al-Islām
– Usool Al Imān
– Mufeed Al-Mustafeed fee kufr tārik At-Tawheed
– Majmu’ Ar-rasā’il fee At-Tawheed wa Al-Eemān
– Masā’il Al-Jāhiliyyah
– Tafseer Kalimah At-Tawheed
– Nawāqid Al-Islām
– Ma’ana At-Taghut
– Kitāb Al-Kabā’ir
– Shuroot As-Salāh Wa Arkānuha Wa Wājibātuha
– Ādāb Al-Mashee ilā Al-Masjid
– Mukhtasar sirāh Ar-rasul
– Mukhtasar Zād Al-Ma’ād

*MUTUWAR SHI*
Shi (Shaykh) Allāh yayi mashi rahama, ya rasu a ranar litinin shekara ta 1206. Allāh ya saka mashi da mafificin alkhairi saboda haƙiƙa Allāh ya tseratar da mutane da yawa daga shirka, Bidi’ah da kaucewa hanya ta hanyar shi da kuma da’awar shi a faɗin duniya.

Taimakon Allāh muke nema

Amincin Allāh ya tabbata akan annabin mu Muhammad da mutanen gidansa da sahabbansa baki ɗaya.

*ƊALIBAN SHI*

Babban Malamin yana da ɗalibai dayawa da suka ɗauki ilimi wajen sa, daga ciki akwai:

1) al-Imām Sa’ud Ibn ‘AbdulAziz Ibn Muhammad ibn Sau’d
2) Ɗan sa, Hussein ibn Muhammad ibn AbdulWahhab
3) Ɗan sa, Abdullāh Ibn Muhammad ibn AbdulWahhab
4) Ɗan sa, Ali Ibn Muhammad ibn AbdulWahhab

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *