Articles - Rubuce-Rubuce

Wajibcin Ɗa’a da Biyayya ga Manzon Allāh

Ka sani cewa lallai Allah ya karrara waɗansu ƙa’idoji ga kowane musulumi. Yana Mai faɗa:

“Kuma dukkan abin da Manzo yazo muku dashi, ku riƙe shi, kuma dukkan abin da ya hane ku, to! ku bar shi, kuma ku bi Allah da taƙawa, lallai Allah Mai tsananin uƙuba ne.”

Haka da faɗinSa:

“Kuma dukkan wanda ya saɓawa Allah da ManzonSa, kuma ya ƙetare iyakokinSa, zai shigar da shi wuta, yana mai dawwama a cikin ta, kuma yana da wata azaba mai wulakantarwa.”

Haka da faɗin Sa:
“Kuma dukkan wanda ya saɓawa Allah da ManzonSa, to! lallai ne an tanada masa wutar Jahannama, suna masu dawwama a cikinta, har abada.”

Haka da faɗin Sa:

“To! Lallai waɗanda suke saɓawa umurninSa, su ji tsoron wata fitina ta same su, ko wata azaba mai raɗaɗi ta same su.”

“Sai dai A’a! (ba haka abun yake ba) Ina rantsuwa da Ubangijin ka, ba za su yi imani ba, sai sun yarda da hukuncinka akan abin da ya saɓa a tsakaninsu, sannan ba su sami wani ƙunci a cikin
zukatan su ba daga abin da ka hukunta, kuma suka sallama,
sallamawa.”

A dalilin haka manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi yace:

“Ina rantsuwa da wanda rai na yake a hannunSa, ɗayan ku bashi da Imāni har sai ya kasance son zuciyar sa ya dace da abinda nazo da shi.”

(al-Bagawi ya ruwaito a cikin Sharhin sa na “As Sunnah” haka An Nawawi a cikin Arba’ūna Hadith da isnadi ingatacce)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *